Hukumomin Saudiyya sun kama wani dan Najeriya daya da ’yan Saudiyya uku bisa zargin safarar hodar ibilis da ta kai nauyin kilogiram 2.2 a kasar.
Sashen binciken manyan laifuka na rundunar ’yan sandan kasar ya ce ya samu nasarar dakile yunkurin shigar da hodar iblis zuwa biranen Riyadh da Jeddah.
- United na da damar kammala Firimiyar Ingila a sahun ’yan hudun farko — Ten Hag
- ISWAP ta kashe manoma 3, ta sace 11 a Borno
’Yan sandan sun ce mutanen hudu sun dade suna aikata laifin safarar hodar ibilis din tare da sayar da ita a cikin kasar ta hanyar amfani da wasu miyagun dabaru.
Jami’an ’yan sandan sun ce za a gurfanar da mutanen a gaban kotu da zarar sun kammala gudanar da bincike.
Safarar kwaya dai babban laifi ne a Saudiyya da za a iya yanke wa mutum hukuncin daurin shekaru masu yawa a gidan yari