Hukumomin Babban Birnin Tarayya sun tabbatar da kama wani babban dan kwangila daga kasar waje kan sace fitilun kan titi.
Dubun dan kwangilar ta cika ne bayan da farko an yi zargin cewa ’yan bola-jari ne suke sace fitilun kan titin.
Kodinetan Hukumar Kula da Birnin Abuja (AMMC), Felix Obuah, ne ya sanar da haka a yayin rangadin aikin gyaran fitilun kan titin da ministan birnin, Nyeson Wike ya ba da umarni.
Duk da cewa Felix Obuah bai bayyan sunan da kasar wajen ko kamfaninsa ba, amma ya ce kamfanin sananne ne, kuma wanda ake zargin zai fuskanci hukunci.
- Yadda ’yan ta’adda suka addabi babban layin lantarkin Arewa
- ’Yan bindiga sun tarwatsa ƙauyuka 23 a sansanin sojoji
Ya bayyana cewa dan kasar wajen da ke tsare a halin yanzu, yana sace fitilun titin ne da nufin a ba shi kwangilar aikin.
Obuah ya ci gaba da cewa a rangadin aikin da suka gudanar, sun gano an sace rukuni 18 daga cikin rukunai 21 na fitilun kan titin, amma a halin yanzu ana aikin gyaransu.