Rundunar ’yan sandan jihar Filato ta kama wani ɗan bindiga a lokacin da yake jinyar raunin harbin bindiga a wani asibiti.
Kakakin rundunar, Alabo Alfred, ya ce ɗaya daga cikin ’yan bindigar da aka kama yana cikin waɗanda suka kai hari a unguwar Zurack da ke ƙaramar hukumar Wase ta jihar.
- Ɓata-gari sun lakaɗa wa masu adawa da Ganduje duka a Abuja
- Sanusi II ne Sarki ɗaya tilo a Kano — Gwamna Abba
Alfred ya ce ’yan sanda sun kashe ’yan bindiga bakwai a wani mummunan farmaki da haɗin gwiwar rundunar DSS da wasu jami’an tsaro suka kai a dajin Bangalala na ƙaramar hukumar Wase.
Ya ƙara da cewa an miƙa ’yan bindigar da aka kama zuwa sashin binciken manyan laifuka na jihar domin gudanar da bincike mai zurfi.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “An kashe ’yan bindiga bakwai a farmakin haɗin gwiwar jami’an tsaro na DSS da wasu jami’an tsaro suka kai a dajin Bangalala na ƙaramar hukumar Wase ta Jihar Filato, mai iyaka da jihohin Filato, Bauchi da Jihar Taraba.
“Sauran ’yan bindigan da suka gudu a yayin farmakin sun kai hari a ƙauyukan Zurak da Dakai, suka kashe mutane tara tare da ƙona gidaje shida.
“Bayan faruwar lamarin, kwamishinan ’yan sandan Filato ya ƙara tura jami’ansa yankin inda ya umarci kwamandan yankin Langtang ya mayar da sansaninsa zuwa ƙaramar hukumar Wase nan take.
“An miƙa wanda ake zargin zuwa sashin binciken manyan laifuka na jiha (SCID), a Jos, domin gudanar da bincike mai zurfi.”