✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kama dan bindiga da makamai a motar haya

An kama shi da bindigogi kirar AK-47 da albarusai kuma ya amsa cewa nashi ne.

’Yan sanda sun cafke wani dan bindiga a hanyarsa ta zuwa dillanci makamai a cikin motar fasinja.

An kama dillalin makaman ne dauke da bindigogi kirar AK-47 da albarusai a Jihar Kogi, wadda ke cikin jihohin Arewa ta Tsakiya da ’yan bindiga suka sha yin garkuwa da mutane da kuma hallaka manyan mutane da dama.

Kakakin ’yan sandan Jihar Kogi, William Aya ya ce “dan bindiga,  dan fashi kuma mai fasa-kwaurin makaman ya shiga hannu,” ne duk da cewa ya boye bindigogin da albarusan a cikin wani buhun da ya sanya a motar hayar.

Ya bayyaa cewa dubun mai fasa-kwaurin makaman ta cika ne a wani binciken ababan hawa da jami’an rundunar suka gudanar a kan hanyar Idah zuwa Ayingba.

DSP Aya ya ce ’yan sanda sun gano bindiga kirar AK-47 guda biyu da bindigar hannu kirar gida guda daya, sai kuma albarusai 41 da mutumin ya boye a cikin motar fasinjar da ta dauko shi.

A cewarsa, da kama makaman dan bindigar bai yi wata-wata ba wajen amsa cewa shi ne mai su, za kuma a gurfanar da shi a gaban kotu da zarar an kammala bincike.

Aya ba wa mutanen jihar tabbacin cewa su ci gaba da gudanar da harkokinsu cikin bin doka da oda, saboda jami’an tsaro na aiki kan jiki, kan karfi domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi  a fadin jihar.