✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama Dahiru Adamu, kasurgumin mai garkuwa da ake nema ruwa a jallo a Abuja

An sanya tukwicin Naira miliyan 20 ga duk wanda ya ba gudunmuwar kamo masu garkuwa da mutanen biyu.

Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja ta kama wani kusurgumin mai garkuwa da mutane,  Sa’idu Abdulkadir wanda ya fi shahara da suna Dahiru Adamu.

Kwamishinan ‘yan sandan Abuja, CP Benneth Igwe ne ya tabbatar wa manema labarai kamun Dahiru Adamu a hedikwatar rundunar a ranar Juma’a.

Ya ce an dai yi musayar wuta tsakanin ’yan sanda da ’yan ta’addan yayin wani samame da suka kai a sansanonin masu garkuwa da mutane da ke iyaka da Jihar Nasarawa da Abuja ta yankin Karamar Hukumar Kuje.

Ya bayyana cewa ’yan sandan sun kai samamen ne da tsakar daren ranar Alhamis, inda bayan ‘yan bindigar sun ankara, suka bude wa ’yan sandan wuta amma daga karshe suka yi galaba a kansu.

CP Benneth ya ce a yayin samamen, an kubutar da wasu mutane biyu — Habu Yakubu da Isufu Abubakar — wadanda aka yi garkuwa da su a kauyen Kwaita na gundumar Pegi da ke Karamar Hukumar Kuje.

“Binciken farko da muka gudanar ya nuna cewa wanda ake zargin shi ne ya kitsa sacewa tare da kashe hakimin gundumar Ketti, Mista Sunday Yahaya Zakwai,” in ji CP.

A cewarsa, kama Dahiru Adamu babbar nasara ce ga rundunar da kuma gwamnatin babban birnin tarayya Abuja, wanda ya ce hakan zai dawo da zaman lafiya a yankin.

CP Igwe, ya yaba wa Ministan Abuja, Nyesom Wike, bisa goyon baya da karfafa gwiwar ‘yan sanda, yayin da ya yi wa jama’a godiya bisa hadin kai da bayanan da suka bayar da suka kai ga kama shi.

Dahiru Adamu a hannun ‘yan sanda

Sai dai ya ce rundunar ‘yan sandan ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin ta kawar da duk wasu masu tayar da zaune tsaye da aikata miyagun laifuka a Abuja, inda ya bukaci mazauna babban birnin kasar da su ci gaba da yin taka-tsan-tsan tare da kai rahoton duk wani motsi da ba su yarda da shi ba ga ‘yan sanda.

“Bincike na farko ya nuna cewa wanda ake zargin shi ne ya kitsa sace tare da kashe wani mai suna Mista Sunday Yahaya Zakwai, hakimin kauyen Ketti.

“Yayin da ake ci gaba da kokarin damke sauran wadanda ake nema ruwa a jallo, CP Benneth ya tabbatar wa masu aikata laifuka a Abuja cewa ba su da wurin buya.

Kazalika, ya bukaci mazauna yankin da su bayar da rahoton abubuwan da ake zargi ta hanyar layukan gaggawa kamar haka; 08032003913, 08061581938, 07057337653, da 08028940883; da 09022222352.

Aminiya ta ruwaito cewa, a ranar Litinin da ta gabata ce tsohon Gwamnan Jihar Ribas Wike ya sanar da sanya tukwicin Naira miliyan 20 ga duk wanda ya ba gudunmuwar kamo masu garkuwa da mutanen biyu.