Rundunar ’yan sandar Jihar Kaduna ta samu nasarar kama wata motar dokon kaya dauke da buhuna 600 na takin zamanin da ake zargin na sata ne.
A kunshin sanarwar da ya fitar, kakakin rundunar ’yan sandan, ASP Mansur Hassan ya ce Kwamishinan ’Yan Sanda Ali Audu Dabigi ya bayar da umarnin kamo motar ce bayan samun bayanan sirri game da lamarin.
- NAHCON ta tsawaita wa’adin biyan kudin Hajjin bana
- Za mu kara soke lasisin wasu masu hakar ma’adanai a bana — Alake
ASP Hassan ya ce bayan samun bayanan sirrin ne aka tura runduna ta musamman wadda ta kama motar a yankin Kawo da ke Kaduna.
Ya bayyana cewa kawo yanzu an cafke direban motar mai suna Abubakar Sani wanda mazaunin Nasarawar Pan Madina da ke gundumar Rigasa ta Karamar Hukumar Igabi.
Kazalika, ya ce sun yi nasarar kama wani da ake zargi mai suna Nasiru Rayyanu mazaunin Rigasa da ke da hannu a lamarin, wanda a yanzu bincike ya yi zurfi a kansa.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, rana ce ta baci a ka kama ababen zargin da takin wadda ake zargin na sata da ake shirin kai wa Zariya domin sayarwa.
Kwamishinan ’yan sanda Ali Audu Dabigi ya roki al’ummar Jihar Kaduna da su ci gaba da ba jami’an tsaro hadin kai tare da goyon baya domin samar da ingantacen tsaro.