✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kama basarake kan zargin kisa a Bauchi

Wani basarake da ake zargi da aikata kisa ya fada a komar ’yan sanda a Jihar Bauchi. Ana zargin basaraken ne da aikata kisa a…

Wani basarake da ake zargi da aikata kisa ya fada a komar ’yan sanda a Jihar Bauchi.

Ana zargin basaraken ne da aikata kisa a yankin Yelwa da ke kusa da birnin Bauchi.

Mai magana da yawun Rundunar ’Yan Sandan Jihar, SP Ahmed Wakil, ya tabbatar da kama wanda ake zargin cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Litinin a Bauchi.

Ya ce ana zargin basaraken ne da kashe wani mutum sakamakon hatsarin mota.

Jami’in ya ce, an dauki batun daga ofishin ’yan sanda da ke Yelwa zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na rundunar da ke jihar don zurfafa bincike.

Bayanai sun ce matasan yankin da lamarin ya faru sun gudanar da zanga-zanga inda suka mamaye babbar hanyar garin Tafawa Balewa da ke jihar don nuna rashin jin dadinsu kan abin da ya faru.

(NAN)