’Yan sanda sun cafke wasu mutum biyu kan satar wayoyi kusan dubu daya a kasuwannin wayoyi da ke titin Beirut da kuma Farm Centre a Kano.
Kakakin ’yan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce an cafke mutanen ne bayan ’yan kasuwannin wayoyin sun kai kara cewa an fasa shagunansu an kwashe musu wayoyi da sauran kadarori na miliyoyin Naira.
- Titunan da ake ginawa yanzu a Najeria ba za su shekara 7 lafiya ba —Minista
- Gwamnatin Kano za ta yi karar alkalin zaben gwamna kan cin mutuncin Kanawa
Ya ce da farko “Wani dan kasuwa a Kasuwar ’Yan Waya da ke Beirut Road ya kawo rahoto cewa an sace wayoyi a shagonsa, kuma yana zargin yaron shagon nasa.”
Jami’in ya ce bayan an tsare yaron shagon, bai bata lokaci ba wajen amsa laifin ya kuma fallasa wanda suka hada baki da wani wajen aikata laifin.
Bayan bincike aka kamo wanda ya taimaka musu wajen boye kayan da suka hada da wayoyi guda 890.
Kiyawa ya shawarci jama’a musamman ’yan kasuwa da su rika hattara game da wanda za su amince wa da dukiyarsu.
Kiyawa ya ci gaba da cewa “Rundunarmu ta samu korafi daga shugabannin Kasuwar ’Yan Waya ta Dansulaika da ke Farm Center, cewa an fasa musu shaguna 11 ta silin an kwashe wayoyi da kwamfutocin kan tebur da laptop da kudaden da suka yi ciniki da katunan ATM da sauran kayayyaki.”
Bayan bincike rundunar ta kamo wani wanda ya amsa cewa shi ne ya aikata, “ya taimaka wa ’yan sanda suka kwato wayoyi 106, laptop 9, kudin da aka yi ciniki N115,940, katin ATM guda 9, da sauran kayayyaki.
“Shi ma ma a gurfanar da shi a kotu.”