Wani saurayi dan kasar Brazil ya shiga hannun ’yan sanda a daidai lokacin da yake tsakiyar bikin murnar zagayowar ranar haihuwarsa.
Saurayin da ya cika shekara 18, ya shiga hannun ’yan sandan ne bisa zargin yin sata.
- Ra’ayi: Yadda talla ke sanadin lalacewar ’ya’ya mata a Arewa
- Mulkin soja ake yi a Kaduna ba dimokuradiyya ba – Isa Ashiru
Zagayowar ranar ya kamata ta zama abar murna, amma ga saurayi Paulo Rodrigo das Nebes, daga yankin Rio Grande do Norte na Brazil, ranar ta zo masa da akasin haka.
Sai dai shi wannan saurayi an kama shi a ranar bayan samun hoton kyamarar tsaro yana satar kayan sauti da sauran bangarorin cikin motocin mutane.
Paulo ya yi bikin zagayowar ranar haihuwarsa a ofishin ’yan sanda tare da ma’aikatan wurin suna rera masa wakar “Barka da ranar haihuwarka!”
Hakazalika, sun taya shi buduri na bayar da kek da lemon kwalba don girmamawa.
Bayanai sun ce abin da ya kara dagula lamuran, shi ne an dauki komai kuma an wallafa shi a yanar gizo.
An ji muryar dan sandan da yake daukar bidiyon cikin raha yana cewa: “Ba za mu iya daga bikin wannan rana ba,” yayin da abokan aikinsa biyu ’yan sandan farin kaya 5 na garin Macau suka taimaka masa wajen shirya tebura don gudanar da bikin.
’Yan sandan da suka halarci bikin sun yi ta rera wakar farin ciki domin taya Paulo murna, sannan sun zuba Koka Kola, har ma sun sa shi ya yanka kek din da suka saya masa.
Bugu da kari, sun kuma bai wa mahaifiyarsa yanka biyu na kek din, lamarin da matashin ya dauka a matsayin wulakanci ko cin fuska.
Bayan bidiyon bikin murnar ya yadu a shafukan sada zumunta, ’yan sandan musamman na Brazil sun ba da sanarwa ga jama’a cewa za a gudanar da bincike.
Haka kuma, sun ce za a dauki matakin ladabtarwa a kan ’yan sandan da suka halarci nuna abin kunyar da aka yi wa Paulo.