An kai wa tawagar dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023 mai zuwa, Alhaji Atiku Abubakar, hari a Maiduguri, babban birnin jihar Borno a ranar Laraba.
A wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta na zamani, an ga mutane na ta kokarin guduwa, yayin da ake harbi a sararin samaniya.
- Rikicin PDP: Akwai fahimtar juna tsakanina da su Wike – Gwamnan Bauchi
- Abin da Hushpuppi ya yi na karshe kafin Alkali ya aike da shi kurkuku a Amurka
Gabanin harin dai, tawagar dan takarar ta isa jihar Borno, daya daga cikin jihohin da APC take mulki, domin gangamin yakin neman zabenta.
Rahotanni sun ce an ga hotunan motocin ayarin dan takarar da aka lalata a filin taro na Ramat da ke Maiduguri.
Sai dai mai magana da yawun Kwamitin yakin Neman Zaben Atikun, Sanata Dino Melaye, ya yi zargin cewa jam’iyyar APC mai mulki ce ta kai musu harin.
Tsohon Sanatan ya kuma yi ikirarin cewa akalla mutum sama da 70 ne yanzu haka ke can kwance a asibiti sakamakon raunukan da suka ji yayin harin.
Ya ce, “Sun so ne su hana mu gudanar da gangamin; maganar da nake yi da kai yanzu haka, akwai mutum 74 da suka ji wa rauni da yanzu haka suke kwance a asibiti.
“’Yan dabar sun kuma lalata mata motoci da dama,” inji Dino Melaye.
To sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoton, jam’iyyar ta APC ba ta mayar da martani ba kan wadannan zarge-zargen.