Shugaban Kasar Afghanistan ya tsallake rijiya da baya daga wani harin bom da aka kai masa a safiyar Babbar Sallah.
Ma’aikatar Harkokin Cikin Gidan Afghanistan ta ce akalla bama-bamai uku ne aka harbo a daidai lokacin Shugaban Kasar zai fara gabatar da jawabinsa na sallah a birnin Kabul da misalin karfe 8 na safiyar Talata.
- An yi yunkurin caka wa Shugaban Mali wuka a filin Idi
- An kai wa masu sayayyar Babbar Sallah harin bom a kasuwa
An ji karar fashewar bama-baman a fadin yankin Green Zone, inda Fadar Shugaban Kasar da ofisoshin jakadancin kasashe suke.
“A yau makiyan kasar Afghanistan sun kaddamar da hare-haren bom a sassa daban-daban na birnin Kabul, inda rokokin suka lalata wasu wurare uku.
“Muna gudanar da bincike domin tabbatar da girman irin barnar da suka yi,” a cewar mai magana da yawun ma’aikatar, Mirwais Stanikzai.
Mintoci kadan bayan harin, Shugaban Kasar ya fara gabatar da jawabin nasa a gaban manyan jami’an gwamnatinsa.
An sha nufar Fadar Shugaban Kasar Afghaninstan da harin bom, wanda na karshen aka kai a watan Disamban 2020.
Harin na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar Taliban ta tsananta kai hare-hare a Afghanistan, inda ake sa ran dakarun kasashen waje za su kammala janyewa a karshen watan Agusta.