✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kai wa Ofishin Jakadancin Saudiyya hari a Sudan

Maharan sun kwace wasu daga cikin kadarorin ma’aikatar.

Wata kungiya da ke dauke da makamai ta yi wa Ofishin Jakadancin Saudiyya da ke Khartoum kawanya.

A cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Saudiyya ta fitar, ta ce kungiyar masu dauke da makamai sun lalata kayan aiki da kyamarori.

Sanarwar ta kuma ce maharan sun kwace wasu daga cikin kadarorin ma’aikatar, tare da lalata na’urori da intanet din ofishin.

Saudiyya ta yi Allah-wadai da kakkausar murya kan wannan aika-aikar tare da yin kira da a tabbatar da mutunta tsarin diflomasiyya ta hanyar hukunta wadanda suka aikita laifin

Masarautar ta sake jaddata kiran dakatar da fada tsakanin sojojin kasar, tare da kawo karshen tashe tashen hankula, da kuma ba da kariya ga jami’an diflomasiyya da fararen hula.