Wata kungiya da ke dauke da makamai ta yi wa Ofishin Jakadancin Saudiyya da ke Khartoum kawanya.
A cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Saudiyya ta fitar, ta ce kungiyar masu dauke da makamai sun lalata kayan aiki da kyamarori.
- Mun cika da mamakin bajintar Haaland — Guardiola
- PSG ta dauki matakin ladabtar da Messi kan kai ziyara Saudiyya
Sanarwar ta kuma ce maharan sun kwace wasu daga cikin kadarorin ma’aikatar, tare da lalata na’urori da intanet din ofishin.
Saudiyya ta yi Allah-wadai da kakkausar murya kan wannan aika-aikar tare da yin kira da a tabbatar da mutunta tsarin diflomasiyya ta hanyar hukunta wadanda suka aikita laifin
Masarautar ta sake jaddata kiran dakatar da fada tsakanin sojojin kasar, tare da kawo karshen tashe tashen hankula, da kuma ba da kariya ga jami’an diflomasiyya da fararen hula.