A ranar Juma’a wasu ’yan bindiga sun kai hari gidan na hannun daman Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, Prince Tonye Princewill, da ke Fatakwal, babban birnin Jihar Ribas.
Ana zargin hayar ’yan bindigar aka yi don ganin bayan Princewill wanda daya ne daga cikin ’yan takarar Gwamnan Jihar karkashin APC a zaben 2023 mai zuwa.
- Isra’ila ta kai hari masallacin birnin Kudus, ta raunata masallata 158
- A farkon 2023 za mu fara tunkudo iskar Gas zuwa Kaduna da Kano – NNPC
Princewill ne ya bayyana harin da aka kai gidan nasa da safiyar Juma’a, yana mai cewa bayan da maharan suka fasa kofa suka shiga gidan kai tsaye, sun nufi dakin da suka yi zaton za su cim masa, amma ba su tarar da shi ba.
Ya ce in ban da matattarar bayanan kyamarar tsaro ta CCTV, babu abin da suka dauka a gidan.
Dan takarar ya yi zargin harin na da nasaba da batun zaben 2023, inda ya ce mai yiwuwa wadanda suka san ba za su kai bantensu ba a zaben ne suka ga dacewar su bi ta wannan hanyar don cim ma manufarsu.
Ya kuma ce “An fasa min gida an shiga da safiyar yau [Juma’a]. A bayyane yake ni aka zo nema, saboda maharan sun tafi ne kai tsaye zuwa dakin da suka yi zaton nawa ne, suka fasa suka shiga amma ba su same ni ba.
“Babu abin da suka dauka face matattarar bayanan da kyamarar CCTV ta nada wanda ya ba ni tabbatacin raina suka zo dauka.”
Ya kuma yi godiya ga Allah kan yadda ya ce da shi da iyalansa babu wanda aka cutar sakamakon harin.
“Ina mai tabbatar wa masoya da magoya bayana cewa wannan abu da ya faru ba zai karkatar da hankalina ba, sai dai ma ya kara min kwarin gwiwa.
“A bayyane yake mun zama kashin makogwaro ga wani da tawagarsa, kuma nan ba da dadewa ba za a san ko wane ne shi. Yanzu dai addu’a da goyon bayanku nake bukata.
“Duk wani Karin bayani da muka samu kan lamarin za mu bayyana komai ta hannun jami’an tsaro. Jami’an tsaro na ci gaba da gudanar da aikinsu, kuma ina da yakin za a yi adalci,” inji Princewill.
Da aka nemi jin ta bakinsa kan lamarin, Kakakin ’Yan Sandan Jihar ta Ribas, Iringe Grace Koko, ya ce ya tuntubi Baturen ’Yan Sandan yankin don jin gaskiyar lamarin.