Wasu ’yan bindiga sun kai hari kan wata motar bas ta sufurin fasinja ta Benue Links da ke kan hanyarta a titin Ikobi na ƙaramar hukumar Otukpo a Jihar Benuwe, inda suka kashe direban da wani fasinja na gaba, yayin da suka yi awon gaba da wasu fasinjojin.
Lamarin ya afku ne da yammacin ranar Alhamis a kusa da rusasshen kamfanin Benue Burnt Bricks, wanda aka fi sani da hanyar shiga garin Otukpo.
- ’Yan sanda sun gayyaci Sarki Sanusi domin amsa tambayoyi
- Motar fasinja ta kama wuta wasu sun tsallake rijiya da baya
Motar mallakar gwamnatin Jihar ta kamfanin Benue Links Nigeria Limited tana kan hanyar Makurdi zuwa Otukpo lokacin da aka yi mata kwanton ɓauna.
A wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na kamfanin, Johnson Ehi Daniel ya fitar a ranar Juma’a, ya tabbatar da faruwar harin, ya kuma yaba da yadda jami’an tsaro suka mayar da martani cikin gaggawa, tare da bayyana ƙwarin gwiwar ci gaba da ƙoƙarin kuɓutar da fasinjojin da aka sace.
“Benue Links Nigeria Limited ta yi takaicin sanar da harin da aka kai kan wata motar safa mai lamba PP512. Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Alhamis, 3 ga watan Afrilu, 2025, kusa da Otukpo Burnt Bricks lokacin da wasu mahara ɗauke da makamai suka yi wa motar kwanton ɓauna.
“Abin takaici, maharan sun harbe direban motar bas mai kujeru 18, Mista Samuel Agege da wani fasinja na gaba, yayin da ’yan bindigar suka yi yunƙurin sace sauran fasinjojin, wasu mutane uku sun yi nasarar tserewa, wani kuma ya sauka tun da farko a garin Taraku kafin faruwar lamarin,” in ji sanarwar.
Hukumomin kamfanin sufurin sun jajantawa iyalan waɗanda suka rasu tare da yin alƙawarin ci gaba da haɗa kai da jami’an tsaro domin ganin an dawo da fasinjojin da aka sace.