Wasu ’yan bindiga da ake zargin ’yan kungiyar IPOB ne sun kai wa jami’an Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) da ke aikin rajistar katin zabe hari a Jihar Enugu.
An kai wa jami’an hari ne mako biyu bayan mahara sun kona Ofishin INEC na Karamar Hukumar Igboeze ta Arewa a jihar ta Enugu
- Hana sayen kuri’u ba aikinmu ba ne —INEC
- Zaben Musulmi da Kirista a baya bai tsinana wa Najeriya komai ba – Oshiomhole
Kwamishinan INEC na Kasa Kan Sadarwa da Wayar da Kan Jama’a, Festus Okoye, ya ce maharan sun far wa jami’an hukumar ne a lokacin da suke tsaka da aiki, inda suka bude wuta babu kakkautawa, suka tarwatsa kowa.
Ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 2.30 na rana a wata makarantar firamare da ke unguwar Umuopu a mazabar Umuozzi ta 19 da ke Karamar Hukumar Igboeze ta Arewa a Jihar Enugu a ranar Laraba.
“A garin guje-gujen ne aka jikkata wani daga cikin ma’aikatan namu, wanda yanzu haka ana jinyar shi a asibiti.
“Injinan rajistar zabe biyu kuma sun bace tare da kayan jami’an namu, har da wayoyinsu.
Idan ba a manta ba, a ranar 3 ga watan Yuli da muke ciki wasu da ba san ko su wane ne ba sun kona ofishin INEC na karamar hukumar.