Wani dan kunar bakin wake ya kai hari kan wata motar bas mai cike da ma’aikatan hukumar zaben ’yan majalisar dokokin kasar Somaliya, inda ya kashe akalla mutum shida a birnin Mogadishu.
An kai harin kunar bakin waken ne da sanyin safiyar Alhamis a lokacin da motar ke wucewa a kan hanyar da ta nufi ofishin shugaban kasar.
- An kashe ladani yana cikin kiran sallah a Zamfara
- NAJERIYA A YAU: Tasirin Harshen Koyarwa Kan Neman Ilimi
Daraktan Hukumar Agajin Gaggawa na kasar, Abdikadir Abdirahman, ya tabbatar da harin, inda ya ce akalla mutum shida sun rasa rayukansu.
Wani jami’in hukumar zabe da ya tsallake rijiya da baya, , Saiido Abdillahi, ya bayyana cewa suna cikin tafiya a mota suka hangi wani ya yi kansu da gudu, amma ’yan sanda suka bude mishi wuta kafin tashin bam din a kusa da motarsu.
Tuni dai kungiyar al-Shabaab wadda ke da alaka da Al Qaeda, ta dauki alhakin kai harin, inda ta ce ta kashe wakilai shida da ’yan sanda biyar a yayin harin.
An fara zaben ’yan majalisar dokokin kasar ne a ranar 1 ga watan Nuwambar 2021, kuma da farko ya kamata a kawo karshensa a ranar 24 ga watan Disamba, amma wasu dalilai suka sanya aka dage zaben.
Amma a halin yanzu ana sa ran kammala shi a ranar 25 ga watan Fabrairu.
Harin kuma da aka kai kan jami’an zaben na iya haifar da wani karin kalubale ga wajen kammala zaben.