✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun kai wa ayarin motocin Buhari hari a hanyar Daura

Wadanda suka jikkata a sakamakon harin na karbar magani.

’Yan bindiga sun kai hari kan ayarin motocin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a yammacin Talatar nan a hanyarsu ta zuwa garin Daura da ke Jihar Katsina.

Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Mallam Garba Shehu ya fitar, ta ce ’yan bindigar sun kai hari kan ayarin motocin ne dauke da jami’an tsaro da sauran hadimai a shirye-shiryen da shugaban kasar ke yi na tafiya Daura domin bikin Babbar Sallah.

Malam Shehu ya ce ’yan bindigar da suka yi wa ayarin motocin kwanton bauna, sun fuskanci tirjiya daga jami’an tsaro da suka hada da sojoji, ’yan sanda da kuma DSS wadanda suka mayar musu da martani.

Sanarwar ta ce biyu daga cikin ya tawagar na karbar magani a sakamakon wasu kananan raunuka da suka samu, inda dukkan sauran ma’aikata da hadiman shugaban kasar suka isa Daura cikin aminci.

Hakan dai na faruwa ne bayan da rahotanni suka ce wasu ‘yan bindigar suka kashe wani Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda a Jihar ta Katsina yayin wani artabu a Karamar Hukumar Dutsinma.

Jami’in, ACP Aminu Umar, wanda kuma shi ne Kwamandan Yanki (Area Commander), ya rasa ransa ne bayan da ya jagoranci wata tawagar ‘yan sanda zuwa wani wuri inda aka bayar da rahoton cewa wasu kungiyoyin ‘yan bindiga sun kashe junansu.

Wasu majiyoyi sun shaida wa wakilin Aminiya cewa da ma dai ‘yan bindigar na jin haushin ACP Aminu Umar saboda ya hana su sakat.

Katsina na cikin jihohin da suka yi kaurin juna wajen hare-haren ‘yan bindiga a shiyyar Arewa maso Yamma ta Najeriya.