Mutum bakwai ake fargabar sun mutu yayin da wasu biyar suka jikkata a wani mummunan hari da wasu ’yan sara-suka suka kai hari kauyen Kurmin Gandu da ke Karamar Hukumar Zangon Kataf ta Jihar Kaduna.
Aminiya kamar yadda wata majiya ta shaida mata ta samu cewa lamarin ya auku ne da misalin karfe 8.00 na Yammacin ranar Lahadin da ta gabata.
- ’Yan bindiga sun kashe mutum 12 da suka fita ceton wani dan kasuwa da aka sace
- Hatsari ya ritsa da ayarin motocin Gwamnan Bauchi
- Salihu Tanko Yakasai: Tsohon Gwamnan Jigawa ya kalubalanci masu magana da yawun Buhari
Majiyar ta ce gugun maharan bila adadin da suka kai harin kwatsam suka shiga far wa mutanen kauyen ba ji ba gani.
Yayin tabbatar da aukuwar lamarin, Shugaban Kwamitin Tsaro da Zaman Lafiya na Masarautar Atyap, Mista John Bala Gora, ya ce maharan sun yi amfani da adduna da wukake wajen sheke ayarsu a kan al’ummar kauyen.
Ya ce tuni aka garzaya da wadanda suka jikkata zuwa Babban Asibitin Zonkwa domin basu kulawa.
Ya kara da cewa, akwai mutanen kauyen da dama da aka nema aka rasa wanda suka ranta a na kare zuwa cikin jeji domin tseratar da rayukansu.
Yayin da Aminiya ta tuntubi jami’in hulda da al’umma na rundunar ’yan sandan jihar Kaduna, ASP Muhammad Jalige domin tabbatar da ingancin rahoton, ya sha alwashin waiwayar wakilinta.