✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kai sabon hari a Yankin Birnin Tarayya

Hari na uku cikin kwana uku da ’yan ta’adda suka kai a Kwali da ke Birnin Tarayya

An yi garkuwa da wani direba mazaunin Yan bindiga sun kai wani sabon hari a Karamar Hukumar Kwali da ke karkashin Yankin Birnin Tarayya.

Harin na uku ke nan cikin mako uku da ’yan ta’adda suka kai a karamar hukumar ta Kwali.

A ranar Lahadi ’yan ta’adda sun kai a unguwar Sheda, wanda katangarsu daya da ya Makarantar Makarantar Sakandaren Gwamnatin Tarayya da ke Kwali, lamarin da ya yi sanadiyyar rufe makarantar.

A wancan harin ne aka yi garkuwa da wasu ma’aurata, Mista Sunday Odoma Ojarume da matarsa Janet, wada daga bayan bisani maharan su sako ta cewa ta nemo musu kudin fansar mijin nata.

Lamarin ne ya sa aka kira iyayen dalibai su je su tafi da ’ya’yansu, daga bayan gwamnati ta rufe daukacin makarantu da ke Birnin Tarayya daga ranar Laraba.

Yada aka kai sabon harin

Wani mazaunin unguwar Chida da ke Karamar Hukumar Kwali, Dangana Musa, ya ce yi garkuwa da wani direba mai suna Atazamu Azaki tare da kwandastansa, Ayuba John, a harin da aka kai unguwar ranar Alhamis.

Ya ce maharan, dauke da miyagun makamai, sun far wa direben da yaron motansa ne bayan sun je daukar kaya ne a wata gona da ake yin gawayin girki.

Ya bayyana cewa daga baya sun sako yaron motar domin ya je ya sanar da iyalan uban gidansa abin da ya faru.

“Sai da suka yi doguwar tafiya da su a kafa kafin suka saki yaron motan cewa ya je ya sanar da iyalan direban an yi garkuwa da shi su kawo kudin fansa,” in ji Musa.

Har zuwa lokacin kammala hada wannan rahoton, kakakin ’yan sanda ta Birnin Tarayya, DSP Adeh Josephine, ba ta amsa rubutaccen sakon da muka tura mata na neman karin bayani game da sabon harin ba.