✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kai mutumin da ya yi wa diyarsa jaririya fyade kurkuku

Kotu ta umarci a tsare wani mutum da ake zargi da yi wa diyarsa mai wata bakwai da haihuwa fyade a gidan yari. Ana zargin…

Kotu ta umarci a tsare wani mutum da ake zargi da yi wa diyarsa mai wata bakwai da haihuwa fyade a gidan yari.

Ana zargin Simon Emeka mai shekara 38 da yi wa jaririyar fyade ne a ranar Litinin, 1 ga watan Yuni.

Alkalin Kotun Majestare da ke zamanta a Makurdi Mai Shari’a Isaac Ajim ya ba da umarnin tsare Simon a kurkuku.

Dan sandan mai gabatar da karar, Sajan Friday Kanshio ya shaida wa kotun cewa wata mata mai suna Josephine ce ta sanar da ‘yan sanda lamarin.

Josephine ta yi korafin ne bayan ta iske mahaifiyar jaririyar mai suna Favour Emeka a asibitin da ta kai ta tana zargin uban diyar ne ya lalata ta.

Ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike, amma wanda ake zargin ya musanta aikata laifin da ake tuhumarsa da aikatawa.

Alkalin kotun ya yi watsi da neman belin wanda ake zargin, sannan ya ba da umarnin a tsare shi a gidan yari har zuwa ranar 31 ga watan Agusta, 2020.