Akalla mutum biyu sun rasu, wasu da dama sun jikkata bayan fashewar bama-bamai a wasu tagwayen hare-hare da aka kai Kampala, babban birnin kasar Uganda.
Hukumomin kasar sun tabbatar da hare-haren, daya a kusa da harabar majalisar dokokin kasar, na biyun kuma a kusa da wani ofishin ’yan sanda.
- Saif al-Islam: Dan Gaddafi zai yi takarar Shugaban Libya
- Sarki Salman da sauye-sauyensa a shekara bakwai a kan mulki
Sufeto-Janar na ’Yan Sandan Uganda, Edward Ochom ya ce, “Tabbas an kai hare-hare amma har yanzu ana kan bincike domin gano wadanda suka dauki nauyinsu.”
Gidan talabijin na kasar, NTV Uganda ya ce tuni aka fitar da mutane daga harabar majaliar bayan harin na safiyar Talata.
“Masu aikin ceto, ciki har da jami’an kungiyar Red Cross na ta kokarin kashe wutar da ta tashi a kan titin shiga Majalisar,” inji gidan talabijin din a shafinsa na Twitter.
Sojojin kasar Uganda sun dade suna yaki da mayakan kungiyar al Shababa ta kasar Somaliya, mai alaka da kungiyar al Qaeda.
Al Shabaab dai ta sha kai hare-haren bom a Uganda, mai yakar kungiyar a matsayin wani bangare na rundunar samar da tsaro da zaman lafiya ta Gamayyar Afirka (AU).
A watan da ya gabata ne kungiyar ta dauki alhakin harin bom na farko da aka kai a wani otal a kasar inda ya kashe wata mai sayar da abinci.
A watan ne kuma ’yan sandan kasar suka sanar da mutuwar wani dan kunar bakin wake a cikin wata motar safa, inda ya raunata mutane da dama.