✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kai harin bom a caji ofis a Anambra

Maharan sun yi awon gaba da makaman caji ofis din bayan artabu da ’yan sanda

Wasu mahara sun kai farmaki inda suka tarwatsa ofishin ’yan sanda da bom a yankin Ihiala da ke Karamar Hukumar Ihiala ta Jihar Anambra.

An zargi maharan sun saki masu laifin da ke tsare a ofishin ’yan sandan a ranar Laraba.

Sun kuma fasa dakin ajiye makamai na ofishin ’yan sandan inda suka yi awon gaba da makamai.

Harin da ya dauki tsawon sa’o’i ana artabu tsakanin ’yan sanda da maharan, ya tilasta mazauna yankin tserewa.

Sai dai har yanzu ba a samu tabbacin samu asarar rai ba a dalilin harin.

Kakakin ’yan sandan jihar, DSP Toochukwu Ikengaz ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce ’yan sanda sun kwato bindiga kirar AK-47 da daya daga cikin maharan ya tsere ya bari.

“A ranar 28 ga watan Disamba, 2022 wasu ’yan bindiga sun kai hari ofishin ’yan sanda na Ihiala, amma an kwato bindiga kirar AK-47 da daya daga cikinsu ya tsere ya bari.

“Maharan sun tsere sakamakon luguden wuta da suka sha daga hannun ’yan sanda.

“Sai dai abun takaici bom din da suka jefa cikin ofishin ya lalata kusa rabin ginin.

“An kashe wutar zuwa yanzu muna ci gaba da bincike a yankin kuma zamu sanar da karin bayani nan gaba,” in ji shi.

Yankin Ihiala da sauran wuraren da ke makwabtaka na fama da hare-haren ’yan bindiga a jihar.

Sai dai jami’an tsaron hadin gwiwa da gwamnatin jihar ta kafa na shiga lungu da sako don ci gaba da yaki da bata-garin.