✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kai hari ofishin Jaridar ThisDay bayan shekara 10 da harin bom

Shekara 10 bayan harin bom, mahara sun kai sabon hari a kamfanin Jaridar This Day

Wasu mahara da ba a san ko su wane ne ba sun kai hari a ofishin kamfanin Jaridar ThisDay da ke Abuja, inda suka yi barazanar aika ma’aikatan kamfanin lahira.

Kafar Labarai ta Arise News, mallakin Kamfanin Jaridar ThisDay, ta ruwaito cewa maharan da suke dauke da muggan makamai sun kutsa cikin harabar kamfanin ne da misalin karfe uku na asuba.

Harin na daren Alhamis zuwa ne shekara 10 bayan harin bom da aka kai wa ofisoshin kamfanin na This ay da ke Abuja da Kaduna.

Bayan shigar maharan cikin harabar kamfanin da ke unguwar Utako a birnin Abuja ne suka tara ma’aikatan a wuri guda, suna barazanar kashe su idan suka kuskura suka sanar da jami’an tsaro.

Arise News ta ambato jami’an tsaron da ke aiki a kamfanin suna cewa kafin tafiyar maharan, sun yi kukarin cewa za su sake dowawa.