✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kai hari a kasuwa a Taraba

Mahara sun kai farmaki kan jama'a a Kasuwar Didango da ke Karamar Karim Lamido da ke Jihar Taraba.

Mahara sun kai farmaki kan jama’a a Kasuwar Didango da ke Karamar Karim Lamido da ke Jihar Taraba.

Wani mazaunin garin, Yakubu Adamu ya shaida wa Aminiya cewa mahara kusan 200 dauke da makamai ne suka far wa kasuwar a ranar Laraba, suka kashe mutum biyu, suka jikkata wasu da dama sunnna suka wawushe kayayyaki na miliyoyin Naira.

Ya ce a yayin da kasuwar ke tsaka da ci a ranar Laraba ne maharan, wadanda ake zargin ’yan sa kan wata kabila ne, suka far mata bagatatan, “ba tare da an tsokane su ba suka far wa Didango, wanda yawancin mazaunansa Fulani, Hausawa, Jarawa da kuma ’yan kabilar Wurkum ne.

Sai dai ya ce matasan Didango su yi arangama da maharan suka fatattake su, a yayin da wata majiya ta yi zargin an kawo musu harin ne domin tayar da rikicin kabilanci a yankin.

Kakakin ’yan sandan Jihar Taraba, SP USman Abdullahi ya tabbatar da harin, amma ya ce mutum daya ne aka kashe.