Masu garkuwa da mutane sun kai hari a gonar tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo, inda suka yi awon gaba da manyan ma’aikata uku.
’Yan bindigar sun yi garkuwa ma’aikatan kamfanin tsohon shugaban kasar mai suna Obasanjo Holdings da ke mahaifarsa ne bayan sun bude wa motar ma’aikatan wuta a yammacin ranar Laraba.
- An cafke motocin abincin ’yan bindiga da mutum 100 a Zamfara
- Matashi ya kitsa sace yarsa kan bashin kudi
Wadanda aka yi garkuwar da su su hada da Jami’in Kula da Kudade da Mai Binciken Kudade da kuma Manajan Adana.
Rahotanni sun ce masu garkuwar sun bi sawun ma’aikatan ne zuwa kamfanin da ke yankin Kobape a Karamar Hukumar Obafemi-Owode ta Jihar Ogun sannan suka yi awon gaba da su.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ogun ta tabbatar da aukuwar lamarin, ta bakin kakakinta, Abimbola Oyeyemi.
“Gaskiya ne hakan ya faru da misalin karfe 6 na yamma; Gonar Obasanjon tana yankin Kobape.
“Amma mun fara neman wadanda aka yi garkuwa da su din kuma muna da kwarin gwiwar cewa za a ceto su cikin koshin lafiya.”