A ranar Lahadin makon jiya ce aka kaddamar da sababbin shugabannin da za su jagoranci kungiyar ’yan asalin kasar Nijar mazauna Jihar Katsina bayan gudanar da zaben da mambobin kungiyar suka yi.
Wannan ne zabe na farko da aka samu canjin shugabanci a sama da shekara 15 da kafa kungiyar a jihar a karkashin jagorancin tsohon shugabanta Alhaji Garba Tumfafi.
Shi dai wannan zabe wanda aka yi ta hanyar sulhu a tsakanin ’yan takara, an gudanar da shi ne gaban karamar Jakadiyar Nijar a Najeriya Madam Rabi’atu Abdu kuma ya gudana cikin lumana.
A lokacin da take rantsar da sababbin shugabannin, Jakadiyar ta ja hankalin al’ummar Nijar mazauna Najeriya su ci gaba da zaman lafiya da sauran jama’a kamar yadda suka saba.
Malama Rabi’atu ta ce “A iya sanina a zamana na karamar Jakadiya a nan Najeriya da ke da ofishi a Kano, ina samun koke-koke da dama daga wasu sassan da ke karkashina amma har zuwa yau ba a taba kawo mini kukan wani dan Nijar daga nan Jihar Katsina ba. Wannan ya kara tabbatar da cewa akwai kyakkyawar fahimta a tsakanin juna.” Da ta juya kan sababbin shugabannin da aka zaba ta ja hankalinsu a kan su sani amana ce Allah Ya ba su ta jama’ar da za su jagoranta, “Daga yanzu ofishina zai yi harka kai-tsaye da kungiya da shugabanninta.”
A jawabin sabon shugaban kungiyar Alhaji Ali Mamane ya ce za su yi iya kokarinsu don ganin sun kawo sauyi mai ma’ana a kungiyar ta yadda za ta tafi daidai da zamani. Sannan ya ce kungiyar za ta yi iya kokarinta don ganin cewa al’ummar Nijar mazauna Jihar Katsina sun yi rajistar da duk ake bukata daga ko’ina a jihar. Sannan ya yi kira ga sauran ’ya’yan kungiyar su ci gaba da zaman lafiya a tsakaninsu tare da hadin kai.
A bayanin Shugabar Matan kungiyar Hajiya Hurera Ibrahim ta ce za ta bullo da wani shiri na inganta rayuwar matan kungiyar da sauran mata ’yan asalin Nijar mazauna Jihar Katsina.
Daga cikin shugabannin da aka zaba akwai Alhaji Ali Mamane a matsayin shugaba. Sai Alhaji Hassan dahiru da Lawal Isa a matsayin mataimaka na daya da na biyu. Abubakar dan Sumba shi ne Sakatare. An kuma zabi Sa’idu Hassan Mai bincike ya yin da Alka Abdu ya zama Jami’in Hulda da Jama’a. A sashen mata kuwa Hajiya Hurera Ibrahim ce ta zama Shugaba yayin da Nana Ammani ta zama Mataimakiyarta sai Zainab Idris Ma’aji da Amina Hamisu a matsayin Jami’ar Hulda da Jama’a.