A ranar Litinin da ta gabata ce aka kaddamar da littafi a kan rayuwar Shugaban kasar Muhammadu Buhari mai taken ‘Muhammadu Buhari: The Challenges of Leadership in Nageria’ a zauren taro na Cibiyar ’Yar’aduwa da ke Abuja.
Tsohon Shugaban kasa, Yakubu Gowon ne ya jagoranci bikin kaddamarwar, kuma ya bayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari mayaki ne, wanda ke aiki tukuru domin ganin ya farfado da tattalin arzikin Najeriya, duk kuwa da irin manyan kalubalen da kasar ke fuskanta.
Littafin, wanda shahararren malamin jami’a, Farfesa John N. Paden ya rubuta, ya kunshi bayanai ne a kan rayuwar Shugaba Buhari da kuma gwagwarmayarsa tun daga shigarsa siyasa zuwa yau. Marubucin, wanda shi ne ya rubuta littafin tarihin marigayi Sardauna Ahmadu Bello, ya bayyana Shugaba Muhammadu Buhari da cewa mutum ne jajirtacce, mai kishin kasa, wanda ke kokarin yin duk wani abu da zai taimaki kasarsa. Ya kara da cewa, ya rubuta littafin ne domin ya bayyana wa duniya ko wane ne Shugaba Muhammadu Buhari.
Tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya yaba wa marubucin littafin, wanda ya ce ya rubuta littafin da inganci. A cewarsa, duk wanda ke son sanin Najeriya da shugabanninta, to ya nemi littafin.
Shugabannin kasashen Chadi da Benin da Nijar da ke makwabtaka da Najeriya sun halarci taron kaddamar da littafin.
Sauran manyan mutanen da suka halarci kaddamarwar sun hada da Mataimakin Shugaban kasa, Yemi Osinbajo da Jagoran Jam’iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Tinubu da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa, Cif Odigie Oyegun da Alhaji Isma’ila Isa Funtuwa da Farfesa Ibrahim Gambari da tsohon Jakadan Amurka a Najeriya, John Campbell.
An kaddamar da littafi kan rayuwar Shugaban kasa Buhari a Abuja
A ranar Litinin da ta gabata ce aka kaddamar da littafi a kan rayuwar Shugaban kasar Muhammadu Buhari mai taken ‘Muhammadu Buhari: The Challenges of…