✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kaddamar da jirgin kasa na farko mai amfani da Hydrogen a Jamus

Wannan dai shi ne karo na farko da aka kirkiri jirgin

Kasar Jamus ta kaddamar da wasu jiragen kasa guda 14 da gaba daya suke amfani da sinadarin hydrogen a maimakon mai a Jihar Lower Saxony da ke kasar.

Kasar ta kaddamar da layin dogo wanda ake sarrafa shi gaba daya ta hanyar  sinadarin na hydrogen.

Wannan kuma wani gagarumin ci gaba ne wajen safarar jiragen kasa duk da kalubalen samar da kayayyakin da ake bukata don gudanar da shi.

Rukunin jiragen kasa 14 da katafaren kamfanin Alstom na Kasar Faransa ya ba wa jihar Lower Saxony ta kasar Jamus, sun maye gurbin motoci masu amfani da dizal a kan titi masu nisan kilomita 100.

Garuruwan da jirgin zai rika zirga-zirga a cikinsu sun hada da Cuxhaven da Bremerhaven da Bremervoerde da Buxtehude da ke kusa da garin Hamburg.

“Muna matukar alfaharin sanya wannan fasaha a cikin aiki tare da abokanmu masu karfi a matsayin sabuwar fasaha ta farko a duniya,” inji Shugaban kamfanin,  Alstom Henri Poupart-Lafarge a cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Laraba.

Jiragen kasa na hydrogen sun zama wata hanya mai ban sha’awa don hana lalata layukan dogo da kuma maye gurbin dizal mai dumama yanayi, wanda har yanzu kashi 20 cikin 100 na harkokin sufuri a Jamus ke amfani da shi.