✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kaddamar da hukumar yaki da masu cin zarafin mata a Borno

Bisa la’akari da yawaitar karuwar cin zarafin mata da wasu ke yi a garin Maiduguri, musamman ma a akasarin sansanonin ’yan gudun hijira da yakin…

Bisa la’akari da yawaitar karuwar cin zarafin mata da wasu ke yi a garin Maiduguri, musamman ma a akasarin sansanonin ’yan gudun hijira da yakin Boko Haram ya raba su da muhallansu, inda ake yawan samun matasa suna yi wa ’yan mata fyade, al’amarin da hukumomi a Jihar Borno suka mike tsaye wajen dakile wannan mummunan lamarin, ta hanyar samar da cibiyar yaki da cin zarafin mata.

Uwargidan Gwamnan Jihar Borno, Hajiya Nana Kashim Shettima ta ce: “Rahotanni na nuni da cewa wannan mummunar dabi’a ta cin zarafin mata tana kara yawaita a wannan jiha tamu ta Borno, a sakamakon rashin tsaron da ya addabe mu, wanda kuma ya haifar da bude sansanoni da dama a cikin garin Maiduguri. A saboda haka ba za mu zauna mu zuba ido mu ga irin wadannan ababe na faruwa ba. A saboda haka, za mu yi iyaka kokarinmu wajen ganin an dakile wannan mummunar dabi’a da ke haifar da munanan halaye a tsakanin al’umma. A don haka ina kira ga kungiyoyi da daidaikun mutane da su mike tsaye wajen fada da wannan al’amari.

Ta ce dalili ke nan ya sanya gwamnati ta shigo da ma’aikatun kiwon lafiya da ta harkokin mata da ta shari’a da kuma hukumomin tsaro, don su hada hannu wajen yakar wannan lamarin.

Uwargidan ta yi kira ga wadanda abin ya shafa kai tsaye da su bai wa hukumomi hadin kai wajen ganin cewar an magance wannan al’amarin. Da ta juya ga gidauniyarta ta SWOT mai tallafa wa marayu, zawarawa da almajirai, ta ce gidauniyar ta tallafa wa gajiyayyu da marasa galihu da marayu.