✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zanga-zanga: An baza jami’an tsaro a Kaduna

Gwamnatin Jihar Kaduna ta baza jami’an tsaro a sassan jihar domin dakile faruwar tashin hankali da zanga-zangar #EndInsecurityNow ka iya haifarwa. Aminiya ta ga yadda…

Gwamnatin Jihar Kaduna ta baza jami’an tsaro a sassan jihar domin dakile faruwar tashin hankali da zanga-zangar #EndInsecurityNow ka iya haifarwa.

Aminiya ta ga yadda aka jibge ’yan sanda da dama a kan shataletalen Gidan Gwamnati da misalin karfe 10 na safe, ranar Talata.

Da farko masu zanga-zangar sun je gidan gwamnatin jihar domin ganawa da Gwmana Nasiru El-Rufai.

Masu zanga-zangar sun sake fitowa ranar da misalin karfe 12 na rana suna kade-kade da wake-waken kawo karshen matsalar tsaro a jihar ta Kaduna, da ma Arewacin Najeriya.

%d bloggers like this: