✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An jefi Shugaban Faransa, Macron, da kwai a tsakiyar jama’a

Macron yana tsaka da gaisawa da jama'a aka jefe shi da kwai.

Wani mutum ya jefi Shugaban Kasar Faransa, Emmanuel Macron da kwai a bainar jama’a, a wata kasuwar baje koli da shugaban ya ziyarta a birnin Lyon na kasarsa.

Mista Macron yana tsaka da gaisawa da mahalarta baje-kolin a karkashin rumfar wani otal ne aka samu wani wanda ya jefe shi da kwai, ya kuma same shi a kafada.

Mutumin ya yi jefar ce a daidai lokacin da Mista Macron yake gaisawa da mutanen da ke karkashin rumfar, suna jinjina masa bisa tallafin da gwamnatinsa ta ba wa bangaren otal na kasar domin rage musu radadin annobar COVID-19.

Sai dai kuma kwan da aka jefi Mista Macron da shi bai fashe a jikinsa ba, ya dai same shi a kafada sannan ya fadi a kasa, daga baya aka ga mutumin da ya jefe shin an tsare shi, an yi awon gaba da shi.

Da yake magana kan jifar sa da aka yi, shugaban na Faransa ya ce, “Idan har (mutumin) yana da abin da yake son ya fada min, to ya zo zan saurare shi, anjima kuma zan je in gan shi.”

Akalla karo na uku ke nan da ake samun mutanen kasar Farasansa da ke yi wa Mista Macron irin wannan cin mutunci a bainar jama’a.

Idan ba a manta ba, a watan Yuni wani mutum ya tsinke shugaban kasar da mari a bainar jama’a a lokacin shugaban yake musafaha da shi a yankin Valence, inda shugaban ya je nuna farin jininsa.

Kafin nan a 2017 an jefi Macron da kwai a lokacin yakin neman zabe a birnin Paris na ksar.