Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar LP, Peter Obi, ya ce wasu bata-gari sun jefe shi har sau biyu bayan kammala yakin nema zabensa a Katsina.
Cikin wata sanarwa da kakakinsa, Diran Onifade ya fitar ranar Talata, ya ce jifan abin Allah-wadai ne.
- An tsinci gawar matashi mai shekara 12 ba wasu sassan jikinsa a Zariya
- An sace yara ’yan gudun hijira kusan 200 a Birtaniya
“Dan takararmu ya jagoranci tattaunawa da mata a jihar, daga na ya wuce taron yakin neman zaben da aka gudanar a filin wasa na Muhammad Dikko.
“Sai dai a kan hanyarsa ta zuwa filin jirgi ne bata-gari suka hau jifan motar da yake ciki, har suka yi mata rotse.
“Mun zaci shikenan amma da muka yi gaba sai da aka sake samun wasu suka jefe motocinmu kan mu isa filin, Allah ya taimaka babu wanda ya samu rauni,” in ji Onifade.
A cewarsa, jifa na biyun ne ya sa suka fahimci shiri ne na ’yan siyasar da a baya suka yi ikirarin yankin Arewa maso Yammacin Najeriya nasu ne ba na Obi ba, amma zuwansa jihar ya nuna akasin haka.
Sai dai Peter Obj ya yaba wa Katsinawan kan yadda suka yi dafifin tarar shi, inda ya bukaci jami’an tsaro su bankado batagarin don hukunta su.