✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An janye dokar takaita zirga-zirgar Adaidata Sahu a Kano

Gwamnatin Kano ta yi amai ta lashe.

Gwamnatin Kano ta sanar da janye dokar da ta haramta wa ’yan babura masu kafa uku da aka fi sani da Adaidaita Sahu zirga-zirga a wasu manyan titunan jihar.

Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da Hukumar Kula da Zirga-Zirgar Ababen Hawa ta Jihar (KAROTA) ta fitar a Yammacin wannan Larabar.

Da yake zantawa da manema labarai a birnin na Dabo, Shugaban KAROTA, Baffa Babba, ya ce sun yanke wannan shawara ce sakamakon la’akari da rashin kammala shirye-shirye daga bangaren kamfanin motocin da zai rika jigilar fasinjoji a manyan titunan.

A cewar Baffa Babba, akwai tsaiko da aka samu na soma ayyukan sufurin daga ranar Laraba, 30 ga watan Nuwamba, a sakamakon rashin isassun motocin bas-bas da za su rika zirga-zirga a kan manyan titunan.

Da wannan uzuri ne Shugaban KAROTAr yake cewa an jingine sabuwar dokar har sai abin da hali ya yi.

Aminiya ta ruwaito cewa, a ranar Talata ce Gwamnatin Jihar Kano ta bakin Hukumar KAROTA ta sanar da hana baburan masu kafa uku bin wasu tituna a birnin, inda ta maye gurbinsu da dogayen motocin safa-safa da ta kawo.