Gwamnatin Tarayya ta sanar da dage dokar kullen da aka kakaba a jihar Kano da nufin hana yaduwar annobar coronavirus.
Sakataren Gwamnatin Tarayya kuma Shugaban Kwamitin Kar-ta-kwana Mai Yaki da COVID-19, Boss Mustapha, ya sanar da hakan ranar Litinin a Abuja yayin jawabin da kwamitin ya saba gabatarwa karo na 38.
Mista Mustapha ya ce sassauta dokar ya kuma shafi wuraren ibada da sauran wuraren taruwar jama’a.
Ya kuma ce matakin na cikin shawarwarin da kwamitin nasu ya ba shugaban kasa don aiwatarwa a cikin makonni hudu masu zuwa.
- Gwamnatin tarayya ta tsawaita dokar kulle a Kano
- ‘Sassauta dokar kulle a Kano ka iya jawo matsala a Najeriya’
Sakataren Gwamnatin ya kara da cewa bayan da ta shawarci shuwagabannin addini, gwamnatin ta kuma amince a sake bude wuraren ibada bisa amincewar kwamitin da gwamnatocin jihohi.
Zirga-zirga tsakanin jihohi
A kan batun zirga-zirga tsakanin jihohi kuwa, Mista Mustapha ya ce, “Har yanzu dokar tana nan daram, sai dai ga masu safarar kayan abinci, albarkatun man fetur, kayan amfanin masana’antu da sauran kayan amfanin yau da kullum don takaita yaduwar annobar.
“Dole ne a samar da man tsaftace hannu a dukkan wuraren taruwar jama’a, sannan a ci gaba da bayar da tazarar akalla mita biyu tsakanin mutane”.
Ya kuma ce za su hada gwiwa da kungiyoyi masu zaman kansu, da masu rike da sarautun gargajiya, da shuwagabannin addini da sauran shuwagabannin al’umma don wayar da kan jama’a kan yadda za a aiwatar da shawarwarin da kwamitin ya bayar.
A makonni biyun da su ka gabata ne dai gwamnatin tarayya ta sanar da tsawaita dokar kullen a jihar Kano.
Zuwa ranar Lahadi dai mutane 954 ne aka tabbatar sun kamu da cutar a jihar, 240 suka warke 45 kuma su ka riga mu gidan gaskiya, kamar yadda alkakuman ma’aikatar lafiya ta jihar suka tabbatar.