✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An horar da ma’aikatan rediyon Katsina don inganta aikin

Ma’aikatan gidan rediyon Jihar Katsina 19, ne suka samu horo na musamman domin kara inganta aiyukansu. Ma’aikatan da aka horar daga sassa biyu na gidan…

Ma’aikatan gidan rediyon Jihar Katsina 19, ne suka samu horo na musamman domin kara inganta aiyukansu.

Ma’aikatan da aka horar daga sassa biyu na gidan rediyon, da suka hada da sashen labarai da al’amurran yau da kullum tare da takwarorin su na sashen shirye-shirye ne suka samu wannan horo na kwanaki biyu a harabar gidan rediyon da ke Sabon Layi a cikin garin Katsina.

Ita dai wannan horaswar, an yi ta ne da zummar zaburar da ma’aikatan ta yadda zasu kara himma tare da kawo sauyi a wajen gudanar da aiyukan na su domin tafiya daidai da zamani.

Alhaji Sani Bala Kabomo Babban Manajan gidan rediyon Jihar Katsina

Kamar yadda Malam Bature Ahmad, wanda yake tsohon ma’aikacin jarida ne a sashen rediyo da kuma talabijin, har ila yau, tsohon Babban Daraktan sashen labarai na ma’aikatar yada labarai ta Jihar Katsina a lokacin mulkin soja ya ce, yana da kyau ya bayar da tashi irin gudunmuwar musamman ga ma’aikatan wannan gidan rediyo wanda ya dauka shi ne kafar da tafi bayar da sahihan labarai.

“Kowane lokaci ina sauraren wannan gidan rediyo, saboda haka naga ya dace in bayar da tawa gudunmuwar ta hanyar horaswa don gyaran wasu kura-kuran da nike ji ana samu nan da can.”

Shi kuwa Babban Manajan gidan rediyon Alhaji Sani Bala Kabomo, ya nuna farin cikinsa akan irin yadda wannan bawan Allah ya amsa kira tare da sauke wani nauyi a matsayinsa na dan jihar.