✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Press To Play

An horar da kudan zuma don gano masu cutar Coronavirus

Ana bai wa kudajen zumar ruwa mai zaki a matsayin tukuici.

Wadansu masu binciken kimiyya sun horar da kudajen zuma, wadanda suke da karancin kanshi, don gano wanda ya kamu da cutar Coronavirus inda suka ce, yin hakan zai iya rage tsawon lokacin da ake jira don samun sakamakon gwaji da ake yi wa mutane.

Sun ce gwaji da kuan zuman a cikin ’yan dakikai zai bayyana sakamakon wanda aka yi wa gwajin.

Yayin horar da kudan zuman, masana kimiyyar na kasar Holland da ke aiki a dakin binciken kwayoyin halittu a Jami’ar Wageningen sun ce sun bai wa kudajen zumar ruwa mai zaki a matsayin tukuici bayan sun nuna musu samfurorin da suka kamu da kwayar cutar COVID-19.

Farfesa Wim van der Poel wanda masanin kwayoyin cuta ne da yake cikin wadanda aka bai wa aikin gwajin, ya ce, “Ba za su samu lada ba bayan sun nuna musu samfurin da ba ya da dauke da cutar.

Bayan sun saba da wannan tsarin gwaji, kudajen zuman za su iya mika kansu ba tare da wata-wata ba don karbar lada lokacin da aka gabatar musu da kwayar cutar.”

Wani mai kiwon kudan zuma ya ce: “Muna tattarawa kamar yadda muka saba da kudan zuman kuma mun sanya tarkon kamo kudajen zuman.”

“Daidai bayan gabatar da ingantaccen samfurin kuma mun gabatar musu da ruwan sukari.

“Kuma abin da kudan zuma ke yi, shi ne ya fadada gano kwayar cutar bayan shan ruwan sukarin.”

Kudajen zuman suna amfani da harsunansu wajen shan kwayar cutar don tabbatar da gwajin wanda yake dauke da kwayar cutar, kamar yadda masu binciken suka sanar.

Amma wani Farfesa da ya yi nazarin kudan zuma da kwari da riga-kafin dabbobi mai suna Dirk de Graaf a Jami’ar Ghent da ke Belgium, ya ce bai ga dabarar da za ta maye gurbin wasu nau’o’in gwajin Kwarona nan gaba ba.

“Dabarar shakar kwayar cuta da kwari ke yi, an yi gwaji da kyau daga ofishin Tsaro na Amurka don gano abubuwan fashewa da guba a shekarun 1990,” inji De Graaf.