Tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu, Jacob Zuma ya koma gidan yari a wani sabon juyi a hukuncin da aka yanke masa kan raina kotu.
Wannan wani sabon juyin waina ne a kan daurin da aka yi wa tsohon shugaban kasar mai shekara 81 kan laifin raina kotu.
- Za mu kashe Bazoum idan aka kawo mana hari —Sojojin Nijar
- NAJERIYA A YAU: Ƙuncin Da Ake Ciki A Kan Iyakar Najeriya Da Nijar
Mista Zuma wanda kotu ta umarci ya koma kurkuku, ya isa gidan yarin Estcourt ne da misalin karfe 6 na safe “aka shige da shi ciki”, in ji jami’an gidan yarin.
Sai dai kuma ba a fi sa’a guda ba, aka sake shi, a karkashin tsarin rage cunkoso a gidajen yari, kamar yadda kwamishinan gidajen yarin kasar, Makgothi Thobakgale, ya sanar.
Ya ce, “Da zuwansa, ab tantance shi,… daga bisani aka sallame shi,” kamar yadda Thobakgale ya sanar da manema labarai a birnin Pretoria.
A watan yuni aka yanke wa Jacob Zuma hukuncin daurin wata 15 a gidan yari saboda kin zuwa ya ba da shaida a gaban kwamitin binciken zargin rashawa da fifita mukarrabansa a lokacin da yake shugaban kasa.
Hukumar gidajen yarin kasar ta daukaka kara, amma kotu ta yi watsi da bukatar a watan Yuli da ya gabata, ta kuma umarce shi ya koma gidan yarin a ranar Juma’a.
Sai dai zuwansa gidan yarin ke da wuya kuma ya ci gajiyar tsarin afuwa ga daurarru marasa hadari, na Shugaban Cyril Ramaphosa.
Minisan Shari’a Ronald Lamola ya sanar cewa fursunoni 24,000 ne za su ci gajiar tsarin.