✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An harbi limami, an sace mamu 18 a Kastina

’Yan bindiga sun bude wa limami da mamunsa wuta a yayin da suke tsaka da Sallah a masallaci a Karamar Hukumar Funtua ta Jihar Katsina.

’Yan bindiga sun bude wa limami da mamunsa wuta a yayin da suke tsaka da Sallah a masallaci a Karamar Hukumar Funtua ta Jihar Katsina.

Maharan sun kuma yi awon gaba da mutum 18 a lokacin da suka yi dirar mikiya a masallacin a yayin da ake Sallar Isha a garin Dangamji a ranar Asabar.

Tsohon Kansilan Gundumar Dangamji, Lawal Maigamji, ya ce, “Yan bindigar sun yi wa masallacin zobe a yayin da ake jam’in Sallar Isha, suka harbi Imam Yusha’u da Hussaini Jamo, sannan suka yi awon gaba da mutum 18 zuwa cikin daji.”

Tsohon Kansilan ya bayyana cewa an yi sa’a mutum hudu daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su a masallacin sun tsere daga hannun ’yan bindigar kafin su kai su maboyarsu.

Ya ce Imam Yusha’u da Hussaini suna samun sauki a asibitin da ake kunyar su.