✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An harbe ’yan IPOB 8 da suka kai hari ofishin ’yan sanda

Jami’an tsaron sun kuma sami nasarar kwace motoci guda bakwai wadanda maharan suka yi amfani da su wajen kawo harin.

Gamayyar dakarun jami’an tsaro a ranar Alhamis da daddare sun harbe akalla ’yan awaren IPOB takwas da suka yi yunkurin kai hari ofishin ’yan sanda na Orlu dake jihar Imo.

Jami’an tsaron sun kuma sami nasarar kwace motoci guda bakwai wadanda maharan suka yi amfani da su wajen kawo harin.

Harin dai na zuwa ne kasa da sa’o’i 24 bayan Abutu Yaro ya kama aiki a matsayin sabon Kwamishinan ’Yan Sandan jihar ta Imo.

Rahotanni dai sun ce an shafe sa’o’i da dama ana musayar wuta tsakanin maharan da ’yan sanda, kafin daga bisani sojojin Runduna ta 34 dake Obinze a birnin Owerri su kawo musu dauki.

Mazauna garin na Orlu da ma kewaye dai sun kasance cikin zaman dar-dar yayin harin.

“Sam ko rintsawa ba mu samu mun yi ba jiya,” inji wani mazaunin yankin da bai amince a ambaci sunansa ba.

An dai yi zargin cewa maharan sun sami nasarar banka wa wata motar silke dake kwanar garin Umuna a garin na Orlu wuta.

Sai dai yunkurinmu na jin ta bakin Kakakin Rundunar ’Yan Sanda na Jihar, Orlando Ikeokwu ya ci tura ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, amma wata majiya daga ’yan sandanm ta tabbatar da faruwar lamarin.

A cewar majiyar, tuni aka kwaso gawarwakin maharan da motocinsu zuwa shalkwatar ’yan sanda ta jihar dake Owerri.

A ’yan makonnin da suka gabata dai ’yan kungiyar sun jima suna kai hare-hare kan jami’n tsaro a jihohin Kudu maso Gabas da dama.