Rundunar ’yan sandan Najeriya ta samu gagarumar nasara a fagen yaki da ta’addanci, a yayin da ta harbe wasu ’yan daban daji shida a wani ba takashi da ta yi a kauyen Garkogo na Karamar Hukumar Shiroro ta Jihar Neja.
Wasu ’yan daban dajin da dama kuma sun tsere da raunuka na harsashin bindiga inda suka bar baburansu a baya.
Rahotanni sun bayyana cewa, ’yan bindigar sun yi kicibus da karshensu a hannun jami’an ’yan sanda da suka yi musu kwanton bauna bayan samun rahoto a kan ayyukan da suke gudanarwa a yankin.
Wakilin Aminiya ya ruwaito cewa, an jibge jami’an ’yan sanda a kauyen na Garkogo ne biyo bayan hare-haren da ’yan daban daji ke kai wa babu kakkautawa.
A ranar Asabar da ta gabata ce aka ruwaito cewa, ’yan daban daji sun harbe wani mutum daya a kauyen, lamarin da ya sanya jami’an ’yan sanda suka daura damarar farautar su cikin gaggawa.
Wata majiya ta bayar da shaidar cewa, take ’yan daban dajin hudu suka mutu, inda daga bisa kuma aka tsinto gawar wasu biyu a wata gona.
Wannan lamari na zuwa ne bayan kisan wasu sojoji biyar da jami’in dan sanda guda daya da ’yan daban dajin suka yi a kauyen Allawa makonni uku da suka gabata.
Sai dai neman jin ta bakin kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Wasiu Abiodun ya ci tura, kasancewar bai amsa kira da sakon kar ta kwana da aka aike wayarsa ba.