Hukumomi a Afghanistan ranar Lahadi sun ce an harbe mutum takwas ’yan gida daya a wani hari da aka kai wani masallaci dake gabashin kasar.
Gwamnan lardin, Zia’ulhaq Amarkhil ya ce harin, wanda aka kai da daren ranar Asabar a birnin Jalalabad dake yankin Nangarhar, an yi ittifakin cewa wani rikici kan wasu filayen ne musabbabinsa.
- Cutar Murar Tsuntsaye: Manoman Kano sun tafka asarar N600m a watanni 2
- Shekara daya da rasuwar Abba Kyari: Me ya sauya a Najeriya?
Kamfanin Dillancin Labaran Faransa (AFP) ya rawaito cewa dukkan mutum takwas din da aka harbe maza ne.
“Yanzu haka muna kan bincike akan harin, amma bayanan farko-farko sun nuna cewa rikici kan wasu filaye ne ya haddasa shi,” inji Gwamna Amarkhil.
Kakakin Rundunar ’Yan Sanda na Lardin Nangarhar, Fareed Khan ya tabbatar da faruwar lamarin.
Harin dai na zuwa ne a daidai lokacin da Musulman kasar, kamar sauran takwarorinsu na kasashen duniya, ke azumin watan Ramadan, wanda galibi a cikinsa maza kan taru da yamma a masallatai domin yin bude-baki.
Kasar dai kan fuskanci hare-haren ramuwar gayya inda iyalai kan dauki fansar wani laifin da aka yi musu kan abokan fadan nasu.
A wasu lokutan ma, wasu iyalan kan shafe gwamnan shekaru suna dauki-ba-dadi da juna ba tare da kawo karshe rikicin ba.