Akalla mutum daya ne aka tabbatar da kashewa, wasu matafiya da dama kuma aka yi awon gaba da su bayan wani hari da masu garkuwa da mutane suka kai a babbar hanyar Kaduna zuwa Zariya.
Aminiya ta gano cewa lamarin ya faru ne a kusa da kauyen Dumbin Rauga, da daren ranar Litinin.
- ’Yan bindiga sun sace likita yana tsaka da aiki a asibitinsa a Adamawa
- Ku daina tsammanin komai daga Buhari – Obasanjo ga ’yan Najeriya
Wata majiya ta bayyana sunan wanda aka kashe din a matsayin Alhaji Sani Dogara, wanda ke hanyar zuwa Zariya daga Kaduna.
Rahotanni sun ce maharan sun shafe tsawon sa’o’i suna cin karensu ba babbaka ba tare da kakkautawa ba.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoton dai Runudunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ba ta magantu ba kan lamarin, sakamakon kakakinta, ASP Mohammed Jalige bai amsa kiran wayar da wakilinmu ya yi masa ba.
To sai dai wani ganau ya shaida wa wakilinmu cewa ’yan bidnigar, wadanda suka zo a motoci, sun kafa shinge ne a kusa da kauyen Tudun Gaude, sannan suka yi amfani da motocin wajen tafiya da mutanen cikin daji.
“Muna gefen hanya lokacin da muka fuskanci motoci na juyowar ba-zata daga hannun Kaduna zuwa Zariya, yayin da wasu kuma ke gudu zuwa cikin daji.
“Mun kuma ga wasu matafiya da dama suna sauka daga ababen hawansu suna fantsama cikin daji a kafa cikin dimuwa,” inji majiyar.
To sai dai majiyar ta ce lokacin da suke guduwa cikin dajin, babu karar harbin bindiga,amma dai daga bisani ya ga gawar mutum dayan da aka harba a kafada.
Shi ma wani wanda lamarin ya rutsa da shi mai suna Bashir, ya shaida wa Aminiya cewa a lokacin da lamarin ya faru, sun hangi motar kamfani Dangote tana ci da wuta, inda suka bazama cikin daji.
Ya ce daga bisani sojoji sun zo wajen, lamarin da ya basu damar dawowa kan kan hanya.
Bashir ya ce maharan sun tare hanyar ne tun da misalin karfe 8:30 na dare, har kusan zuwa karfe 11:00 suna cin karensu ba babbaka
Wurin da lamarin ya faru dai na da nisa kilomita 15 daga Zariya.