Jami’an ’yan sanda sun samu nasarar harbe wasu masu garkuwa da mutane biyu a Unguwar Hausawa da ke yankin Naharati a Karamar Hukumar Abaji ta birnin Abuja.
Aminiya ta samu cewa masu garkuwar sun yi gamo da karshensu a yayin wata musayar wuta da jami’an ’yan sanda da kuma ’yan bijilanti da ke aikin sintiri a yankin.
- ’Yan bindiga sun sake kai hari makaranta a Kaduna
- Sojoji sun dakile yunkurin kai hari kusa da filin jirgin sama na Kaduna
Wani mazaunin unguwar mai suna Suleiman, ya ce da misalin karfe 1:00 na daren Lahadi ne ’yan bindigar suka yi wa wasu gidaje na Unguwar Hausawa dirar mikiya.
Ya ce gabanin zuwan jami’an tsaro ’yan bindigar tuni sun yi awon gaba da mutum hudu a wasu daga cikin gidajen da suka shiga.
Daga cikin wadanda aka sace akwai Abdullahi Umar, Abdulkarim Yusuf, Abubakar Umar da wani dan shekara 13, Abdulrahman Isah.
“Sai suka fara harbe-harbe a iska domin su razana jama’a bayan sun dauke mutum hudu,” in ji shi.
Shugaban Karamar Hukumar, Alhaji Abdulrahman Ajiya, ya tabbatar da faruwar lamarin na sace wasu daga cikin jama’arsa da kuma harbe wasu ’yan bindigar biyu.
Wakilinmu wanda ya kai ziyara ofishin ’yan sanda, ya gane wa idanunsa gawar masu garkuwar biyu da aka harbe, inda kuma wasu mazauna yankin suka rika tururuwar daukan hoto da bidiyon gawawwakin nasu.
Sauran ababen da aka samu tare da ’yan bindigar da aka harbe akwai layukan waya, wayoyi da kuma layu.
Yayin da aka tuntubi Kakakin rundunar ’yan sandan Abuja, ASP Maryam Yusuf ta inganta rahoto.
Ta ce jami’ansu sun yi bajintar dakile harin wanda a cewarta maharan biyu da aka harbe sun mutu ne a yayin da ake yunkurin kai su Asibiti.