Rahotanni daga Jamhuriyyar Dimokradiyyar Congo sun bayyana cewa, an harbe wani babban malamin addinin Islama yana tsaka da jan Sallar Tarawi a Arewacin Kivu.
An yi wa Sheikh Ali Amini ruwan harsashi yayin da yake jagorantar sallar Asham ranar Asabar a babban masallacin garin Beni.
- An harbe Kwamishina, an yi awon gaba da shugaban Karamar Hukuma a Kogi
- Ramadan: Kungiya ta tallafa wa masu karamin karfi 550 da kayan abinci a Kano
Sheikh Amini ya shahara wajen da’awar hani kan riko da tsattsauran ra’ayin addinin Islama a wani gidan Rediyon kasar.
Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya ruwaito cewa, ’yan tawayen ADF sun kashe akalla mutum 19 ciki har da sojoji 10 bayan Shugaban Kasa Felix Tshisekedi ya ayyana yi wa wasu lardunan kasar biyu kawanya da jami’an tsaro.
Hare-haren baya bayan nan sun faru ne da sanyin safiyar Asabar inda wasu ’yan bindiga suka kai kari kan wasu kauyuka biyu yankin Benin a Arewaci Kivu kamar yadda mahukunta suka tabbatar.
Yawaitar hare-hare daga mayaka masu dauke da makamai da rikice-rikice a tsakanin kabilu a gabashin kasar ya hallaka mutum fiye da 300 tun farkon wannan shekara kawo yanzu.
Hakan na zuwa ne a yayin da sojojin gwamnati da na Majalisar Dinkin Duniya ke kokarin daidaita yanayin a kasar.