Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kai hari kauyukan ’Yar Doka da Kongo dake gundumar Magami cikin Karamar Hukumar Gusau a Jihar Zamfara.
Mazauna yankin sun ce wasu gungun ’yan bindigar sun kutsa kai yankin da sanyin safiyar ranar Laraba sannan suka afka musu.
- Har yanzu ba mu san adadin daliban da aka sace a Jami’ar Greenfield ba – Gwamnatin Kaduna
- Majalisar Dattawa ta amincewa gwamnati ciyo bashin $1.5bn da €995
Wani Mazaunin kauyen ’Yar Doka mai suna Babangida ya ce kimanin wata guda kenan da suka kauracewa gidajensu tun bayan wani hari da ’yan bindigar suka kai yankin.
Ya ce, “Sun kai hari yankin kuma sun bankawa rumbun adana abincin mutane wuta.
“Mazauna yankin a kwanakin baya sun yi hijira zuwa makwabtansu wani gari da ake kira Magami, kimanin kilomita 7 daga yanmacin yankin nasu.
“Sun yanke shawarar komawa garin nasu kwanan nan, ashe ’yan bindigar na shirin sake kai musu hari.
“Yanzu haka sun bar wannan kauyen zuwa wani kauyen na daban.
“Naga raunuka da dama a jikin mazauna yankin, yanzu haka suna nan suna karbar magani.
“’Yan-sa-kai sun yi iya bakin kokarinsu na kawo musu dauki a kauyen na amma duk da haka abin ya ci tura,” inji Babangida.
Sai dai yunkurinmu na ji ta bakin Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, SP Muhammad Shehu ya ci tura har zuwa lokacina hada wannan rahoton.