Wata rundunar hadin gwiwa ta jami’an tsaro a Jihar Ekiti ta harbe wani da ake zargin mai garkuwa da mutane ne a wurin karbar kudin fansa.
Rundunar ta harbe wanda ake zargin ne yayin da ya je karbar kudin fansar wasu mutum biyu da aka yi garkuwa da su a wani dajin da ke tsakanin iyakar Jihohin Ekiti da Kwara.
- An kashe mutum 3 a rikicin ’yan sanda da masu Keke Napep a Legas
- An ceto ma’aikatan Jami’ar Abuja da aka sace
Aminiya ta ruwaito cewa, rundunar hadin gwiwar da ta kunshi sojoji, ’yan sanda da ’yan sa-kai da Sarkin Fulanin Ekiti, Alhaji Adamu Abashe ya kafa, sun kashe mai garkuwa da mutanen a dajin Eruku da ke Jihar Kwara.
Wannan nasara ta samu ne yayin da rundunar ta yi wa gungun masu garkuwa da mutanen kwanton bauna da suka sace wasu mutum biyu.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, tun da farko masu garkuwa da mutanen sun bukaci a biya su fansar Naira miliyan 2.1 da mutanen da ke tsare hannunsu,
Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jihar Ekiti, Sunday Abutu, ya inganta rahoton.
A yayin da yake yi wa manema labarai hole gawar mai garkuwa da mutanen da aka harbe a Babban Ofishin yan sanda da ke Ado Ekiti a ranar Alhamis, Abutu ya ce an samu nasarar ceto mutanen biyu da aka yi garkuwar da su.