✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An harbe kanin Sowore har lahira

Mai Sahara Reporters ya ce an kashe kaninsa a hanyarsa ta dawowa daga jami'a.

Wasu wadanda ba a san ko su wane ne ba sun harbe Olajide Sowore, kanin Omoyele Soware, shugaban kafar Sahara Reporters mai labarai ta intanet, har lahira.

Omoyele ya sanar ta shafinsa na sadar da zumunta cewa an kai wa Olajide Sowore hari aka kuma bindige shi ne a lokacin da yake dawowa daga Jami’ar Igbinedion da ke Okada, a Jihar Edo.

“An harbe kanina wanda na sha nono na bar wa, Olajide Sowore, har lahira a yau din nan a kusa da Okada, Jihar Edo.

“Ana zargin masu garkuwa da mutane ko makiyaya ne suka kai masa harin a lokacin da yake dawowa da Jami’ar Igbinedion a Jihar Edo, inda yake karatu a fannin hada magunguna,” inji shi.

Mutuwar ta kanin nasa, Olajide Sowore, na ta daukar hankali a kafafen sadar da zumunta.