An harbe wani jami’in hukumar tsaro ta DSS har lahira a Owerri, babban birnin Jihar Imo ranar Talata.
Lamarin na zuwa ne kasa da sa’o’i 48 bayan an kone ofishin hukumar da ke garin Nnewi na Jihar Anambra.
- Majalisa ta yi barazanar kama Buba Marwa da Monguno
- Yadda mai juna biyu ta shirya garkuwa da kanta a Yobe
Wakilinmu ya gano cewa jami’in, mai suna Nwachinaemere Ezemuony Ozuzu, wanda dan asalin garin Umuoyo ne a Karamar Hukumar Owerri ta Yamma a Jihar, an harbe shi ne a kan hanyar Owerri zuwa Onitsha.
Rahotanni sun ce ya gamu da ajalin nasa ne lokacin da yake dawowa daga Anambra bayan an tura shi wani aiki, jim kadan da kone ofishin na Nnewi.
Har yanzu dai babu cikakkun bayanai kan kisan, a daidai lokacin da wasu bayanan masu cin karo da juna suke cewa wani alburushin daya daga cikin abokan aikinsa ne ya kashe shi bisa kuskure.
Daya daga cikin iyalan jami’in, Daniel Opara, wanda ya tabbatar da lamarin ya bayyana shi a matsayin abin takaici.
Ya ce, “Har yanzu ba mu sami cikakken bayanin kisan nasa ba, kamar yadda ake zargin cewa wai harsashin wani dan sanda ne da ke tare da wasu abokan aikinsa ne da ke aiki a Anambra.
“Iyalansa na zargin siyasar aiki ce, saboda kwanan nan aka yi masa karin girma.
“Ya fara aiki ne shakara biyar da suka wuce, kuma yana da aure da yara hudu,” inji Daniel.
Kakakin ’yan sandan Jihar, CSP Mike Abattam bai sami amsa wayar wakilinmu ba don jin ta bakin rundunarsu kan harin.