Wata Babbar Kotu ta haramta zanga-zangar tsadar rayuwa a Accra, babban birnin ƙasar Ghana.
TRT ta ruwaito cewa kotun ta hana ƙungiyoyin farar hula gudanar da zanga-zanga a babban birnin ƙasar, kamar yadda ɗaya daga cikin masu shirya zanga-zangar ya bayyana.
- Mutum 4 sun mutu, 16 sun ji rauni a hatsarin mota a Bauchi
- An sanya ranar zaɓen ƙananan hukumomin Kano
Mai shari’a Abena Afia Serwa ce ta amince da buƙatar dakatar da zanga-zangar kamar yadda ’yan sandan ƙasar suka buƙata.
’Yan sandan sun gabatar wa kotun hujjar cewa ba su da isassun jami’an da za su bai wa masu zanga-zangar kariya sakamakon an kai wasu jami’an wuraren tarukan siyasa.
Lamarin dai na zuwa ne a yayin da Gwamnatin Ghana ta bi sahun ƙasashen Afirka wajen ƙoƙarin daƙile zanga-zangar da matasa ke yi kan tsadar rayuwa.
Waɗanda suka shirya gudanar da zanga-zangar a tsakanin 31 ga watan Yuli da kuma 6 ga watan Agusta, sun bayyana cewa zanga-zangar za ta jawo sama da mutum miliyan biyu a kan tituna domin neman Shugaba Nana Akufo-Addo ya ɗauki mataki kan cin hanci da rashawa.
A halin yanzu ana fama da guguwar zanga-zanga wadda ke kaɗawa a faɗin ƙasashen Afirka a ’yan makonnin nan.